Jarirai 12 sun mutu sanadiyar gobara cikin asibiti

Jarirai 12 sun mutu sanadiyar gobara cikin asibiti

–Wasu yan Jarirai 12 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin gobara da ya faru a asibiti.

–Wani mashawarcin ma'aikatan kiwon lafiya yace jarirai 20 ne a cikin asibitin lokacin sal da gobarar ta fara

–Rahotanni sun ce wutan lantarki ne sanadiyar wutan

–Gobarar ta  fara cikin dare kuma an kwashe sa'a 3 kafin aka kashe

Jarirai 12 sun mutu sanadiyar gobara cikin asibiti

Jarirai 12 sun rasa rayukan su a ranan laraba,10 ga watan agusta a wata gobarar wuta da ya faru birnin bagdadi,kasar Iraq. Game da Reuters, bakwainan sun mutu ne asibitin yarmuk a cikin asibitin lokacin gobaran. Wani mashawarcin ma'aikatan kiwon lafiya, Dr Amir Al-Muktar yace jarirai 20 a cikin asibitin lokacin da gobaran ya fara cikin dare, ya kara da cewa wutan ya ja asaran dukiyoyi da dama.

Kakakin ma'aikatan, Ahmed al- Roudani ya ce da yiwuwan witan lantarki ne sanadiyar gobaran.

KU KURANTA : Gwamnati za ta soma kwace gidajen masu laifi a Lagos

Diraktan asibitin, Saad Hatem Ahmed, ya fada ma kafan labarai cewa an dauke mata 29 da jarirai 8 daga asibitin zuwa wani asibiti. Hussein Umar ya rasa yan biyu ,namiji da mace da aka haifa makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel