An soki Koci Samson Siasia bayan Columbia ta ci Najeriya

An soki Koci Samson Siasia bayan Columbia ta ci Najeriya

An soki Koci Samson Siasia bayan Columbia ta ci Najeriya.

Mutanen Najeriya sun zargi Kocin kasar, Samson Siasia da laifi asarar da Kasar ta samu a wasan kwallon kafa a Gasar Olympics da ake bugawa a Birnin Rio na Kasar Brazil. Kasar Columbia ta ba Najeriya kashi ne a wasan karshe na zagayen farko. Idan ba a manta ba Kocin ya bayyana cewa zai ajiye wasu yan wasan su huta (a wasan Columbia) saboda su samu karfin buga zagaye na gaba da kyau, ganin yayi nasarar zuwa mataki nag aba bayan ya buge Japan da kuma Sweden. Kasar Columbia kuwa ta kacaccala Najeriya kana ta ci ta har biyu da nema, hakan ya ba Kasar ta Columbia damar isa mataki na gaba a Gasar. Mutanen Kasar ta Najeriya kuwa, wannan abu bai masu dadi ba, ga abin da wasu daga cikin magoya bayan Kasar ke fada a shafin twitter na zamani:

Owodeinde Olawale ya fara da cewa:

Yanzu sai mu ga kuma ko wa Siasia zai zarga, Minista Dalung mai ‘yar jar hula? - @waleowodeinde

Shi kuwa Erahomol cewa yake yi:

Dole fa Siasia ya dinke barakar da ke bayan Najeriya, bini-bini sai ka ga kwallo ta wuce. - @erahomo

Drakeson ya rubuta:

Sai ka ga Samson Siasia ana wasa kamar wani dan daba… - @luking900

Tundey yana magana kan cewa:

Idan har wannan dan wasa Akpeyi ya taba kwallo, sai kayi ta tunani ko ya aka yi Siasia ya ma taho da shi Gasar #Rio2016. - @realtundey

Owodeinde Olawale ya kara cewa:

Wai shin ta yaya aka yi ma Najeriya ta ci wasannin ta na farko ne? Ya kamata fa Siasia ya tsawatawa yaran nan! - @waleowodeinde

Aroloye A. yace:

Koci Siasia ya kara tabbatar da cewa dai bai san komai ba. A yau baa bin da yayi na dabaru sai shirme. - @adetolaa_a

KU KARANTA: KOCI SAMSON SIAISIA ZAI BAR AIKI?

Idan ana neman irin wadannan sakonni sai a duba filin twitter da lambar #COLNGR, za a ga abin da mutanen Kasar suka yi ta fada dangane da wasan.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel