Makiyaya sun kashe Kiristoci a jihar Kaduna

Makiyaya sun kashe Kiristoci a jihar Kaduna

-Wasu da ake zargin Fulani Makiyaya ne sun kai hari ga Kiristoci a jihar Kaduna

-Ana zargin makiyayan da kashe kimanin Kiristoci 13

-Sun kuma hargitsa cocina uku

Makiyaya sun kashe Kiristoci a jihar Kaduna

Akwai rahotannin cewa wasu musulman Fulani makiyaya sun kai hari ga tarin kauyukkan Kiristoci a jihar Kaduna. Makiyayan sun kai harin ne a makon da ya gabata, sun kashe kimanin Kiristoci 13 sun kuma hargitsa mambobin Cocina uku.

Wani da ya da kyar a harin ya bayyana wan Morning Star News cewa Makiyayan sun kashe mata Kirista guda biyu a kauyen Ninte a ranar Litinin 1 ga watan Augusta. Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa ta san Kiristoci takwas da aka kashe a Gada Biyu a ranar Talata, 2 ga watan Augusta.

KU KARANTA KUMA: Sultan na Sokoto ya shawarci Buhari da ya lura da halin da mutane ke ciki

Jaridar Local newspapers ta ruwaito cewa an kashe mutane tara (9) a Gada Biyu, tare da wasu mutane biyu (2) da aka kashe a Akwa’a a ranar Laraba, 3 ga watan Augusta. Daya daga cikin daruruwan Kiristocin da suka fito daga yankin, Martha Yohanna na cokin Alheri Baptist a kauyen Gada Biyu, ta fada ma Morning Star News cewa harin da aka kai Ninte da Gada Biyu, Musulman Fulani makiyaya ne suka kai harin.

Tace: Washe garin ranar, Fulani makiyaya sun kashe Kiristoci takwas a Gada Biyu, tare da wasu da aka gane mutun biyar, Friday, Akoro, Mamman, Danladi da kuma Jerry.

Asali: Legit.ng

Online view pixel