Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)

Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki a lokacin gamuwa na yan majalisa wato Federal Executive Council (FEC) a ranar Laraba 10 ga watan Augusta.

Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)

Bikin na rantsar da mai bashi shawara na musamman a harkan tattalin arziki, Dr. Adeyemi Dipeolu ya faru ne a majalisar dake fadar shugaban kasa, a babban birnin tarayya Abuja.

Buhari wanda ya shugabanci gamuwar, ya kuma kaddamar da wasu masu bashi shawara na musamman guda hudu (4) da kuma sakatare daya.

KU KARANTA KUMA: Yadda Buhari ya taimaka gurin ceton MTN daga fatara

Ga sunayensu a kasa:

1.Mai bada shawara na musamman a harkan zamantakewar zuba jari, Mrs Maryam Uwais.

2.Mai bada shawara na musamman a al’marin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu.

3.Mai bada shawara na musamman a kan tsare-tsare, Tijani Abdullahi.

4.Sakatare, Ma’aikatar harkokin waje, Ambasa Rafiu Enikanolaye.

A lokacin, an mayar da Uwais, Ojudu da Dipeolu ofishin mataimakin shugaban kasa, an kuma mayar da Abdullahi Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na kasa baki daya.

Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)
Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)
Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)

A jiya munci cewa Shugaban kasa Buhari yayi nadi mai muhimmanci inda ya nada Tosan Erhabor daga Kudancin Najeriya a matsayin shugaban kungiyar likitoci na the Medical Laboratory Science Council of Nigeria (MLSCN).

Asali: Legit.ng

Online view pixel