PDP sun zargi Osiomhole da almubazaranci da kudi

PDP sun zargi Osiomhole da almubazaranci da kudi

-Jam’iyyar PDP babin jihar Edo sun kalubalanci Gwamna Adams Oshiomhole da ya bayyana wa jama’ar jihar Edo mamalakin wani kidan baki, da kuma wani gida wanda ya kai kimanin naira billiyan 5.8 a hanyar Okoro-Otun

-Zargin cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihar, Godwin Obaseki ya karba naira billiyan 1.5 a matsayin kason san daga cikin bashin billiyan 30 da gwamnatin jihar ta karba

-Sun bukaci yan kasuwa dake fuskantar matsaloli saboda ninkayar haraji na gwamnatin jihar da su hada jam’iyyar APC kuri’unsu a ranar 10 ga watan Satumba

PDP sun zargi Osiomhole da almubazaranci da kudi
Adams Oshiomole

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun zargi Gwamna Adams Oshiomhole da almubazaranci da kudi.

Har ila yau Jam’iyyar ta zargi dan takaran gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar, Godwin Obaseki, da karban kudi naira billiyan 1.5 a matsayin kason sa na bashin kudin da jihar ta karba domin aiwatar da aikin ruwa a garin Benin.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta gama ziyararta na kasar Amurka, zata dawo Najeriya (Hotuna)

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Dan Orbih, wanda ya daukaka zargin a ranar Talata 9 ga watan Augusta, ya kalubalanci gwamnan jihar da ya bayyana wa mutanen jihar Edo, mamalakin tsohon gidan saukan bakin Guiness, wanda ke hanyan Reservation na Benin, da kuma wanda ya gina wani gida da aka kiyasta cewa zai kai kimanin naira billiyan 5.8 a hanyan Okoro-Otun.

Orbih yayi kira gay an kasuwa wanda yace suna fuskantar matsaloli sakamakon ninka kudin haraji na gwamnatin jihar da kada su jefa kuri’unsu ga jam’iyyar APC a ranar 10 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel