Tsokacin Mourinho game da dawowar Pogba Man utd

Tsokacin Mourinho game da dawowar Pogba Man utd

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Man utd dake kasar ingila Jose Mourinho ya bayyana dalilin da yasa ya dage akan lalle sai ya siyo dan wasan nan Paul Pogba daga kungiyar Juventus.

Tsokacin Mourinho game da dawowar Pogba Man utd
Jose Mourinho

Shi dai dan wasan ya kafa tarihi ne a matsayin dan wasan da yafi kowa tsada a duniyar kwallo bayan da ya kammala dawowar sa tsohon kulob din sa na Man utd daga Juventus akan kudi sama da £100m.

Dan wasan mai shekaru 23 ya bar kungiyar ta Man utd ne dai akan kudi £1.5m a shekara ta 2012 amma kuma sai gashi ya dawo akan wadannan makudan kudaden da suka zarce kudin da kungiyar nan ta Real madrid ta siyo Gareth Bale akan £85m a shekara ta 2013.

Mourinho yace: "Paul daya ne daga cikin yan wasan da suka fi kowa shahara a duniya don haka ko shakka babu zai taimaka wa kungiyar ta Man utd. Yana da sauri, karfi sannan kuma yana zura kwallaye tare da karantar kwallo cikin kankanin lokaci fiye da yan wasa da dama ciki hadda ma wasan da suka girme shi."

Mai horar war ya cigba da cewa: "A matsayin sa na dan shekaru 23 yana da damar da zai kasance wanda yafi kowa shahara a wurin da yake bugawa nan da shekaru da yawa masu zuwa. Kuma ko shakka babu zai kara habaka tare da ci gaba cikin shekarun 10 masu zuwa."

Pogba dai ya koma ne kungiyar Juventus shekaru 4 da suka wuce inda ya buga kwallo sau 124 yakuma zura kwallaye 28.

Dan wasan na tsakiya har ilayau ya buga wa kasar sa ta Faransa wasanni 38 kuma ya zura kwallaye 6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel