Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal

Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal

Yaron daya daga cikin gaggagga shuwagabannin jam’iyar APC Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya angwance a ranar 8 ga watan agusta. Ba kamar yadda wasu rahotanni suka nuna ba, a jihar legas aka daura auren ba Italy ba.

Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal

Seyi ya auri matarsa Layal J Holm ne a fadar sarkin legas Oba Akiolu dake yankin Iga Idunguran na tsibirin jihar Legas da misalign karfe 11 na safe.

Shugaba Buhari ya aika ma ma’auratan sakon taya murna, inda ya basu shawara da su rike ma juna amana kuma su zauna lafiya. A ranar auren Layal na sanye ne da fararen tufafi da farin hula, shi kum Seyi na sanye da tufafi masu launin shudi

Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal

Manyan baki da suka halarci bikin sun hada da uban Ango, Bola Tinubu, gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, mataimakiyar gwamnan jihar Legas Idiat Adebule, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma sarkin Ife Oba Ogunwusi, sarkin Legas, sarkin Oyo Oba Lamidi Adeyemi.

Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal
Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal
Auren Oluwaseyi Tinubu da amaryarsa Layal

Asali: Legit.ng

Online view pixel