Suleiman Hashimu ya tafi aikin Hajji

Suleiman Hashimu ya tafi aikin Hajji

Suleiman Hashimu wanda ya taka daga Lagos zuwa Abuja a kasa sakamakon don murnar cin zaben da Buhari ya yi, ya samu zuwa hajj.

Hakan ta bayyana ne a shafin sada zumunda da muhawara na Facebook na Suleiman, a inda ya lika sanarwar samun yin aikin hajjin, tare wani hotonsa kusa da wata motar jif kirar Totota Land Cruiser Prado.

Suleiman Hashimu ya tafi aikin Hajji
Suleiman Hashimu a lokacin da ya iso Abuja daga Lagos a kasa a 2015
Suleiman Hashimu ya tafi aikin Hajji
Suleiman Hashimu na shirin zama ALHAJI a 2016

A shafin na sa ya rubuta “Salamma ‘yan uwa da abokan arziki. Da yardar Allah a yammancin yau ne zan tafi zuwa kasa mai tsarki domin yin aikin Hajji. Ina mai rokon gafararku ga duk wanda na batawa. Da fatan za ku samu a addu’arku domin mu je lafiya, mu kuma dawo lafiya. Wassalam.

Suleiman Hashim dai ya yi wani tattaki na tarihi tun daga Lagos zuwa Abuja a ranar 20 ga watan Agustan Shekarar 2015, domin cika alkawarin da ya dauka na yin hakan, idan Muhammadu Buhari ya ci babban zaben da aka gudanar na shekara 2015, duk da kokarin da ‘yan uwa da abokan arziki suka yi na hana shi.

Suleiman yi tattakin ne a inda ya bi ta tsohuwar hanyar zuwa Legas, a inda ya samu babbar tarba a duk garuruwan da ya bi akan hanya, da kuma a lokacin da ya iso Abuja.

A baya-bayan nan, wasu rahotannin na cewa Suleman ya yi da na sanin yin tattakin, saboda halin da talaka ya ke ciki na matsi a yanzu, amma ya wasu rahotanni suka ce ya karyata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel