Dan wasa Paul Pogba ya iso Gidan Old Trafford na Man Utd

Dan wasa Paul Pogba ya iso Gidan Old Trafford na Man Utd

 

– Yanzu haka Pogba yana Gidan Old Trafford inda ake gwajin lafiyar sa.

– Kafin zuwa ranar Laraba 10 ga wannan watan, za a kammala komai.

– Idan har dai wannan ciniki ya yiwu, to Pogba zai zama mafi tsada a tarihin duniyar kwallon kafa.

Dan wasa Paul Pogba ya iso Gidan Old Trafford na Man Utd

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Bafaranshen dan wasan tsakiyan nan, Paul Pogba ya samu isowa gidan Old Trafford na Man Utd domin kammala komowar sa Kungiyar daga Juventus. Paul Pogba dai za ci ma Man Utd kudi akalla ba a kasara ba fam miliyan £89, wannan zai sa dan wasan ya zama mafi tsada a kaf tarihin kwallon kafa a duniya. BBC ta rahoto cewa dan wasan ya kamo hanyar Man Utd ne bayan ya hawo jirgi da Garin Nice, an hange sa a filin saukar jirgi na Manchester a ranar Litinin, jiya. Daga nan ne dan wasan ya wuce filin koyan wasan Kungiyar na Man Utd. Idan har komai ya yiwu, za a kammala sayen dan wasan kafin Ranar Larabar nan.

KU KARANTA: PAUL POGBA ZAI KOMA MAN UTD

Cinikin Paul Pogba zai tasan ma fam miliyan 105 na EURO, da kuma wasu yan kuci-kucin kudi da ba za a rasa ba dada. Duk da dai har yanzu, Man Utd ba ta cin ma yarjejeniya da tsohon dan wasan na ta ba, amma da alama kusan kamar anyi-an gama ne, muddin aka duba lafiyar jikin sa. Kungiyar Man Utd dai ta saye yan wasa uku wannan kakar, sun hada da Zlatan Ibrahimovic, da kuma Henrikh Mkhitaryan, sai Eric Bailly. Dan wasa Paul Pogba ne zai zama na hudu.

Idan dai har aka sayo Paul Pogba, to zai kere Gareth Bale da aka saya daga Tottenham zuwa Real Madrid a 2013 kan kudi fam miliyan £85 tsada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel