Minista Dalung ya bada hakuri danagane da makarar Dream Team Olympics

Minista Dalung ya bada hakuri danagane da makarar Dream Team Olympics

 

– Salomon Dalung ya nemi afuwa game da isar Kungiyar Dream Team VI ta Najeriya a makare.

– Ministan wasannin Kasar ya yabi yan wasan kwallon kafar.

Minista Dalung ya bada hakuri danagane da makarar Dream Team Olympics

Solomon Dalung, Ministan wasanni na Najeriya, ya ba yan wasan Kasar hakuri game da matsalar da aka samu wajen zuwan su Birnin Rio na Brazil domin Gasar Olympics. Minista Dalung ya kalli wasan Najeriya da Sweden a Garin Manaus a Ranar Lahadin nan, inda ya ba yan wasan hakuri bayan an tashi wasan game da abin da ya faru. Bayan ya gaisa da jami’an, Ministan ya bada hakuri game da duk abin da ya faru a hanya. Yace a matsayin sa na Shugaba, dole ya dauki nauyin duk abin da ya faru karkashin sa. Ya kuma yi farin cikin da suka mance da hakan ma ya taba faruwa, suka dage wajen abin da ya kawo su. Dalung yace sun sa Kasar alfahari, ganin sune Kasar farko ta suka isa zagaye na gaba a Gasar.

KU KARANTA: NAJERIYA TA BUGE KASAR SWEDEN A GASAR OLYMPICS

Ministan ya kuma tabbatar ma yan wasan da sauran ma’aikata cewa za a biya su duk wani albashin su da alawus. Ministan dai yana tare da wani Jakadar Kasar ne, Adamu Emozozo, da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar wasanni na Kasar, Chinyeaka Ohaa. Kungiyar dai ta fuskanci irin wannan kalubale a bara wajen cin Kofin U-23 na Nahiyar Afrika a Kasar Senegal. Kyaftin din Kungiyar, Mikel Obi ya kuma bayyanawa Ministan cewa za su yi bakin gwargwado wajen ganin sun lashe kyautar gwal a Gasar.

Kocin Kungiyar Kasar, Samson Siasia dai yace za su bi sannu-sannu har ganin sun yi nasara a Gasar. Ya kuma yi alkawarin ganin ya gyara bayan shi, domin kuwa kusan ta nan ne kadai Kungiyar ke da rauni.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel