Bitar wasu muhimman labarai na ranar Litinin a Jaridu

Bitar wasu muhimman labarai na ranar Litinin a Jaridu

 Ga wasu labaru da jaridun ranar Alhamis 9 ga watan Agusta suka mayar da hankali a kai

Bitar wasu muhimman labarai na ranar Litinin a Jaridu
Wasu labaran da jaridun ke dauke da su na ranar Lahadi

Rayuwata na cikin hadari –Tsohon shugaba Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya koka dangane da barazanar da wasu tsagerun yankin Niger Delta ke yi ga rayuwarsa, saboda bayyana rashin goyon bayansu ga ta da kayar bayan da suke yi a kasar.

Rio 2016: Najeriya ta doke Sweden a kaiwa ga na kusa da na kusa da na karshe

Kungiyar ‘yan wasan Najeriya a gasar tsalle-tsalle da guje-guje na Olympics da ake yi a Rio ta Brazil, sun doke Sweden a gasar kwallon kafa a rukunin B. Hakan ya basu damar zawu mataki na gaba.

Ku kalli wanda zai jagoranci yaki da tsagerun Niger Delta

Gwamnan jihar Bayelsa Dickson Seriake ya bayyana wani tsohon mai gwagwarmaya da makamai Africanus Ukparasia (wanda aka fi sani da General Africa) a matsayin wanda zai jagoranci yaki da tsageru masu fasa butun mai a yankin.

Wasu bayanai masu jan hankali a sabon faifai bidiyon Shekau

Abubakar Shekau fitinannen shugaban Boko Haram, a wani sabon faifan hoton bidiyo da aka yada a ranara Lahadi 7 ga watan Agusta, ya sha alawashin ci gaba da yaki a yayin da ya yi watsi da rarrabuwar kan kungiyar sakamakon nadin wani sabon shugaba da IS ta yi. Rundunar sojin Najeriya dai na ikirarin samu galaba a kan kungiyar.

Tsageru a basajen kayan fastoci sun yi hallaka sojoji

A kalla sojoji uku ne masu aikin kar-ta-kwana a yaki da tsageru, ake zargin wasu tsagerun na Niger delta sun hallaka a Nembe da ke jihar Bayelsa a lokacin da suka yi shigar masu wa’azin Krista.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel