Mutane 16 sun kone kurmus a hadarin mota

Mutane 16 sun kone kurmus a hadarin mota

–An samu wata mumunan hadarin mota a hanya Lokoja zuwa Abaji a Jihar Kogi

–Mutane 16 suka rasa rayukansu sanadiyar wannan hadari motan

–Mutanen da ke cikin motan sun kone kurmus.

An ranan juma’a ne ,5 ga watan agusta Mutane 16 ne suka kone kurmus sanadiyar wata mumunan hadarin motan da ya faru a hanyar Lokoja-Abaji da ke jihar Kogi. Wata motan haya ta samu hadari yayinda tayi kicibis da wata moa a kauyen Alewu .

Mutane 16 sun kone kurmus a hadarin mota

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa mutum daya ne ya tsira a hadarin da ya faru a motan Toyota Hiace da ke nufin zuwa Jihar Kano. Majiya ta fada cewa hadari ya faru ne sakamakon sabawa dokokin hanya. Kwamandan FRSC a Jihar Kogi , Mr. Ugboma Ugochikwu, yayinda yake tabbatar da faruwan hadarin  ,ya fada ma manema labarai a ranan lahadi cewa an birne mutane a wurin da hadarin ya faru.

Yace mutum dayan da ya tsira a hadarin, ya samu kananan raunuka kuma an sallame shi daga asibiti.

Yace : “Hadarin ya faru misalin 6:30 na safe a ranar juma’a a kauyen alewu, a babban titin lokoja- abaji . ta faru yayinda wata motan hanya cike da mutane mai zuwa daga jihar legas kuma nufin jihar kano ta yi kicibis da wata mota mai zuwa daga Abuja zuwa jihar Edo.

KU KARANTA : Likita ya manta da tawul a cikin wata mata.

“Motocin biyu ne suka ci karo,wannan kuma ya faru ne sanadiyar mota daya daga cikinsu da ta saba dokan tuki. Hakazalika gudu na cikin sanadin faruwan hadarin,amma dai hakikanin sanadiyar shine saba dokokin tuki. Hadarin ta jawo fashewa ,wanda mutane 16 suka rasa rayukan su . sun kone ne wuce misali. An birne su a kauyen.  Mutum dayan da ya tsira , an kais hi asibitin koton-karfe,kuma anyi masa jinya ,an sallame shi.

A wata labara mai kama da haka, jaridar daily trust ta samu cewa akalla mutane 5 ne suka rasa rayukan su a wata hadarin motan da ya faru a tashan yaba da ke kauyen gada biyu,a hanyar Abuja-Lokoja da yamman ranar talata ,21 ga watan Agusta. An samu cewan mutane 9 a cikin motan sun samu raunuka kala-kala, jami’an FRSC sun kais u asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel