Hajj 2016:Buhari Ya Kaddamar Da Tashin Mahajjata.  

Hajj 2016:Buhari Ya Kaddamar Da Tashin Mahajjata.  

-Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Tashin mahajjata Najeriya Daga Sokoto Zuwa Kasar Saudiya Na Aikin Hajjin 2016.                          

 -Shugaban Kasar Ya Gargadi Mahajjatan su Kasance Masu Bin Doka.  

 -Sarkin Musulmi Ya Roki Mahajjata Da Suyi Wa Shugaba Buhari Addu'a.        

Hajj 2016:Buhari Ya Kaddamar Da Tashin Mahajjata.  

          

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashin mahajjatan kasar nan na shekara ta2016 daga Sokoto zuwa kasar saudiya ranar 8,Agusta 2016. Jaridar Nan ta rohoto cewa"Gwamnan sokoto Aminu Tambuwal ya wakilci shugaban kasar. Ya bayyana cewa"gwamnatin tarayya tana kokarin dai-daita kasar nan dan jin dadin kowa.

Lokacin da yake bayani gurin kaddamar war" shugaban kasar yace"muna aiki tukuru na kawo dakoki da tsare-tsare dan jin dadin mutanen kasar nan,har da ma wadanda za'a haifa nan gaba. Ya karfafa ma ma'aikatan hukumar aikin hajji (NOHCON) su zama masu jajircewa dan kula da jindadin mahajjatan kasar nan.

An kuma ba mahajjatan shawara da su zama masu bin doka,suyi hakuri da junansu,su zamo wakilai na gari ga iyalansu da kasa baki daya.Sarkin musulmi Alhaji Sa'adu Abubakar III ya roki nahajjatan da su ma shugaba Buhari addu'a a kan jagorancin kasar nan,kuma ya roke mahajjatan da suyi addua'a kan dorewar zaman lafiya da hadin kai da addu'ar yayewar wahalhalun da yan kasar nan suka tsinci kansu.

KU KARANTA : Aikin Hajjin bana : Saudiyya ta hana shiga da Goro

Haka ma,ma'aikatar sufurin jiragen sama NAF tace"A kalla mahajjata 80,000 za'a kwashe nan da sati 5 a filayen jirage 17 a fadin kasar nan. Kungiyar ma'aikata 52 daga NAHCON wanda ya hada har da masu kula da lafiya sun bar kasar nan tun juma'a kan shirye-shiryen aikin hajji na 2016.

Asali: Legit.ng

Online view pixel