Hajji 2016: Buhari ya kaddamar da tashin alhazai a Sokoto

Hajji 2016: Buhari ya kaddamar da tashin alhazai a Sokoto

-Shugaba Buhari ya kadddamar da jigilar alhazi zuwa kasa mai tsarki na bana

-Shugaban kasa ya gargadi alhazai da su bi doka da oda

-Sarkin Musulmi ya yi kira a gare su da yiwa Buhari addu’a

Hajji 2016: Buhari ya kaddamar da tashin alhazai a Sokoto
Wakilin shugaban kasa Aminu Tambuwal ya na mikawa wasu alhazai fasfo a bikin kaddamarwar

A ranar Litinin 8 ga watan Agusta ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar ta jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da Hajjin bana a filn jirgin sama na Sokoto.

Hajji 2016: Buhari ya kaddamar da tashin alhazai a Sokoto
Wakilin Buhari Aminu Tambuwal tare da Sarkin Musulmi da kuma gwamnan jihar Kebbi

Kamfanin dillacin labarai na Nigeria NAN, ya rawaito cewa gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ne ya wakilci shugaban a bikin da ya samu halartar manya baki daga cikin da kuma wajen jihar.

Hajji 2016: Buhari ya kaddamar da tashin alhazai a Sokoto
Alhazai na shiga jirgi domin tafiya kasa mai tsarki a bikin kaddamarwar

A jawabinsa a bikin kaddamarwar, shugaba Buhari ya ce, “a shirye muke don gabatar da shirye-shirye masu nagarta da za su inganta rayuwar ‘yan Najeriya wanda kuma za su amfani ‘ya ‘ya da jikoki”.  Sannan shugban ya yi kira ga jami’an hukumar kula da mahajjatan Najeriya ta kula ‘yan kasar yadda ya kamata a yayin aikin hajjin.

Ga mahajjatan kuma, shugaban ya yi kira a gare su da kiyaye dokin kasa mai tsarki da yin hakuri da junansu tare da kasancewa jakadu na gari ga iyalansu da jihohinsu da kuma kasar baki daya.

A nasa jawabin, Mai alfarama Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, kira ya yi ga alhazan da su yiwa shugaban kasa addu’a, da kuma kasar ta yadda za a samu zaman lafiya da karuwar arziki.

Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya ta ce, kimanin alhazai 80,000 ne za su tashi zuwa kasa mai tsarki a cikin makwannin 5 a filayen jiragen sama 17 na kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel