Wani dan sanda da jami’ar NSCDC sun mutu

Wani dan sanda da jami’ar NSCDC sun mutu

-Wani mutumi jami’in dan sanda da masoyiyar shi wacce jami’ar NSCDC ce sun mutu a jihar Anambra , wata mutuwar fuji’a.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa matan mai suna ifeoma wacce take da ‘ya’ya biyar ,shi kuma mutumin na da yara 3. Rahoto ya nuna cewa an same su a mace ne a ranar lahadi ,7 ga watan yuli,a cikin wani gida a  Ezinifite Okpuno, karamar hukumar Awka ta kudu a jihar Anambara. Iyalan mutumin mazauna Jihar Legas ne ,ita kuma matan yar garin awka ce.

Wani dan sanda da jami’ar NSCDC sun mutu
motar gawan

Ifeoma ta fada ma mijinta cewa zata je coci addu’an dare ne ashe karuwanci ta tafi yi gidan namiji. Wata majiya ta fada ma Jaridar Punch cewa :

 “Matan ta kasance a dakin dan sanda tsawon dare, wani ma’aikaci mai yi ma dan sandan aiki ya zo da safe domin yin aiki sai ya gan su a mace. Ma’aikacin sai ya fito a guje ya sanar da makwabta, sai wani makwabcin ya kulle gidan saboda kada mutane su cika gidan.

Wasu makwabtan da jaridar punch ta yi hira da su sun ce kilan hayakin janareto ne ya kasha su.

“Muna jin karan karamar janareta tsawon dare. Amma misalign karfe 4 na dare, sai janaretan yam utu;kila mai ne yak are. Dan sandan mazaunin gidan ne , bai cika zama ba,amma duka sanda ya zo ,kowa na sani saboda yana kunna janareton sa har wayewar gari. Mutane na kiranshi da ofisa na amma ina tunanin sifeto ne, wani makwabci ya fada.

KU KARANTA : Ga fa hotunan wata mata maishekaru 59 da ta samu ciki

Yan kallo da yan  ta’aziyya sun zo ranan lahadi suna tattaunawa akan faruwan. An ce kanin dan sanda ne mai gidan. Amma daga baya yan banga da yan sanda da jami’an NSCDC sun tarwatsa cinciridon mutanen da ke wurin saboda sun ki wucewa har sai sun ga gawawakin. Daga baya yan sandan suka dauke gawawwakin cikin wata motar daukan gawa .

Kakakin jami’an yan sandan jihar yace. ASP Nkeiru Nwode yace: “Maganan gaskiya shine mutumin ba jami’in yan sanda bane kuma har yanzu bamu san wacece matan ba . ban samu cikakken labara akan al’amarin ba . duk sanda na samu cikakken labara zan fada muku dan Allah

Asali: Legit.ng

Online view pixel