An kama yara masu siyar da kan kwarangwal

An kama yara masu siyar da kan kwarangwal

Dubun wasu kananan yara su hudu ya cika bayan rundunar yansanda ta jihar Akwa Ibom ta kama su da laifin siya da siyarwa na kwarangwal din kawunan mutane.

An kama yara masu siyar da kan kwarangwal

Jami’i mai magana da yawun hukumar yansandar jihar Delia Nwawe yace jami’an sirri na hukumar yansanda ne suka kama yaran bayan sun samu labara daga yan bangan yankin. Shugaban gungun yaran mai suna Emmanuel Edet Ikot ya musanta zargin da ake musu, yace shi dai tsintar kwarangwal din yayi a wani kango bayan mai kangon ya bashi aikin nome ciyayin kangon.

Emmanuel yace “wani mutum ne ya bani aikin nome ciyayi ne a wani kango a Oron, a yayin da nake noman ne nayi karo da wani kwarangwal. Daga nan sai nayi wuf na je fada ma abokaina, sai muka dauki kwarangwal din muka yanke shawarar siyar das hi, amma bamu san wanda zamu siyar ma wa ba.

Daga nan muka yanke shawarar mu kai ma wani boka a Mbo zai iya siya. Mu hudu dukkan mu ne muka nufi Mbo, muna hanya sai wani shugaban yan banga ya kama mu, da ya ga kan kwarangwal din sai ya kira yansanda su kama mu, abin da ya faru kenan, amma ban taba siyar da wani sassan jikin mutum ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel