Wani mutum ya aurar da ‘yar shi mai shekaru 6

Wani mutum ya aurar da ‘yar shi mai shekaru 6

Wani mutum ya aurar da yar shi mai shekaru 6 da haihuwa ga wani mutum mai shekaru 55 saboda an bashi ‘yar akuwa da kayan masarufi. Yayinda aka samu labarin, an aurar da gharibol a wani gari a kasar Afghanistan, yan sanda sun kama ango, seyed ,mai shekaru 55 da haihuwa.

Wani mutum ya aurar da ‘yar shi mai shekaru 6
lokacin da akayi aure

Mahaifin gbarigbol ya aurar da yar shi zuwa ga Seyed, an samu rahoton cewa ya bayar da ita ne da musayan yar akuya da aka bashi da kuma kayayyakin masarufi irinsu shinkafa, shayi, siga, da man girki. A cikin binciken da aka gudanar ne mahaifin Garibgol ya bayyana cewa ya dade yana cikin mawuyacin halin ciyar da iyalinsa, ya aurar da ita ne saboda ya samu sauki kuma ya samu kayan abinci.

A wata bidiyon da Fawad Ahmady ya dauka, an nuna cewa an kama mahaifin Gharibgol a wani kauye ne yayinda mata suka mai dukan tsiya saboda zalunci da ya ma yar sa. Mahaifin yace ya aurar da ita a bisa alkawarin da mutumin yayi na cewa ba zai kwanta da it aba sai ta kai shekara 18.

Seyed ,wanda sananne mutum ne a unguwar ya kai sabuwar amaryan shi gidan yan uwa da ke Firozkoh,a yankin Ghor, yana cewa ‘yar sa ce. Yan uwan suka fara nuna damuwarsu yayinda ya fara tube ta da daddare.

KU KARANTA : Fasto yayi ma wata mata fyade

Da aka tambaye shi cewa anya kuwa wannan yar shi ce, sai ya bada amsa yana cewa matar sa ce,wai mahaifinta ne ya bashi ita. Dan uwan na shi sai ya fada ma wani abokinsa wanda ya kira masu kare hakkin mata a yankin Ghor. “ gwajin asibitin da aka dauka ya nuna cewa ba’ayi lalata da it aba.

An ajiye gbarigbol a wani wuri tare a mahaifiyarta yayinda ake cigaba da gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel