Jonathan ya gana da Kaunda na Zambia

Jonathan ya gana da Kaunda na Zambia

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da tsohon shugaban Zambia kuma daya daga cikin tsaffin shugabannin Afrika da ake girmamawa, Mista Kenneth Kaunda. Jonathan ya gana da shi ne a ranar Asabar 6 ga watan Agusta.

Jonathan ya gana da Kaunda na Zambia
Kenneth Kaunda a lokacin da ya ke tarbar Jonathan a gidansa

Shugaban kasa na farko na daya daga cikin kasashen da ke kudancin Africa, Kenneth Kaunda ya karbi bakuncin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan a gidansa.

Jonathan ya gana da Kaunda na Zambia
Goodluck ya sha kaye a zaben shugaban kasa a Najeriya yana kan karagar mulki

Reno Omokri tsohon hadimin Jonathan a kan kafofin yada labarai na zamani ne, ya yada hotunan ziyarar tsohon shugaban zuwa gidan na Kaunda.

Shugaba Jonathan ya bar Najeriya zuwa Zambia ne a ranar juma’a 5 ga wata, a inda ya ke shugabantar wata tawagar mutane 56 a karkashin hukumar tarayyar Africa, a inda za su sa ido a zaben da za a gudanar a babban zaben kasar.

Jonathan ya gana da Kaunda na Zambia
Tsohon Shugaba Kaunda ya kai shekara 91 da a duniya. Ya dangana tsawon ransa ga dogaro da Ubangiji da kuma kyautatawa makwabta

Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana farin cikin su a shafukan sada zumunta da muhawara na Twitter kan ziyara da kuma ganawar tsaffin shugabannin biyu.

Kenneth Kaunda ya jagoranci gwagwarmayar kwatar ‘yancin kasar daga hannun Turawan mulkin mallaka, a inda yazama shugaban kasar a shekarar 1964, ya ci kuma ci gaba da rike shugabanci har shekara ta 1991.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel