Ra'ayi: Mutanen Igbo Su Bayyana Su Sakarkaru ne Ba Jarumai Ba. 

Ra'ayi: Mutanen Igbo Su Bayyana Su Sakarkaru ne Ba Jarumai Ba. 

Rubutun Edita:1 daga cikin masu karanta labaran Legit.ng Ibeawuchi Aja,ya bayyana ra'ayinshi akan rikicin da ke faruwa a yaankin kudu maso gabashin Najeriya,marubucin ya dora ma shugaban kasa Buhari laifi dan tura sojojin da yayi su shawo kan matsalar.

Bana tunanin mutanen Igbo su kyale tsaagerun Neja Delta a halin da ake ciki. Shugaban kasa ya yanke shawarar tura fulanin sojoji a yanki kudu maso gabashin kasar. Kuma ina tunanin rashin adalci ne da rashin tausayi,in duk yan majalisu masu wakiltar yankin a majalisar dattawa da ta wakilai zasu nade hannu ,su zura ido,suyi zaman su Abuja,aika aikar tana cigaba. Maganar gaskia ita ce mun zabe su ne dan su kwato mana incin mu, kungiyar tsagerun na Neja Delta sun bada sharadi na asaki Nnamdi Kanu

Yanzu zan iya yadda ba mu zabi sakarkaru su wakilce mu ba in duk wanda muka zaba ya fito ya nuna rashin amincewarshi. Ina so in tunatar da shugaban kasa cewa ya karya dokar kasa,dokar da aka rubuta a cikin kundin mulkin kasar nan, ko dai ya fara sasantawa da tsagerun ko su cigabaa.Muna da shugaban kasa wanda be dauki kudu maso gabashin Najeriya mutane ba,nasan yan kudu maso kudu basu yarda da junansu ba,amma ya kamata Igbo su samu  goyon bayan mu, in haka ne kuwaa zamu fito muyi zanga-zanga dan mu nuna mu jarumai ne ba sakarkaru ba.

KU KARANTA : Jigo a MASSOB ya ce Najeriya ta cancanci rabuwa

Abubuwan da aka bayyana a cikin wannan rubutun na ma rubucin ne kuma be zama dole ya wakilci tsarin tace labarai  na Legit.ng ba.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel