Makircin cire gwamna Ikpeazu cin amanar kasa ne - PDP

Makircin cire gwamna Ikpeazu cin amanar kasa ne - PDP

-Wani jigon PDP, Chief Emmanuel Iwuanyanwu, ya dora laifi kan INEC, jami'an tsaro da wasu ma'aikatan shari'a kan hannun da suke dashi a kokarin cire Okezie Ikpeazu a matsayinsa na Gwamnan jihar Abia

-Yayi kira ga hukumar harkokin shari'a (NJC) da ta binciki hukuncin da mai shari'a Okon Abang na kotun tarayya ya bayar kan karar Okezie Ikpeazu

-Ya zargi mai shari'a Okon Abang da kokarin jefa jihar Abia cikin rudu

Makircin cire gwamna Ikpeazu cin amanar kasa ne - PDP
Abia state governor, Okezie Ikpeazu

Jam'iyyar PDP ta bayyana kokarin cire Okezie Ikpeazu a matsayin gwamnan jihar Abiya dalilin hukuncin wata babbar kotun tarayya a matsayin cin amanar kasa Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wani jigo a cikin kwamitin amintattu (BOT) na jam'iyyar Chief Emmanuel Iwuanyanwu, ya ambata haka yayin da ya kai ziyara ga gwamna Ikpeazu a gidan gwamnati dake Umuahia

KU KARANTA : Wani shugaban jam’iyar APC Femi Adeyemi ya rasu

Yayin da jigon jam'iyyar ke dora laifi kan INEC, jami'an tsaro tare da jam'an shari'a a hannun da suke dashi na kokarin cire gwamnan, ya ci gaba da cewa: "Nazo a matsayina na jagorar kabilar Ndi Igbo domin in taya ka murna, zan yi magana a kan halin da muke ciki yanzu, Abin ya gigizamu ace wai wani alkali a Abuja zai zartar da hukunci na cire ka daga ofis

"A wasu kasashe, wannan cin amanar kasa ne, kuma duk masu hannu a ciki ya kamata a tuhumcesu da cin amanar kasa. Abu ne wanda ya kamata yaje gaban kotun daukaka kara, daga nan kuma zuwa kotun koli, amma cikin gaggawa INEC ta amince da hukuncin da ke iya jefa jihar Abia cikin tashin hankali, Ba mamaki wadansu ke cewa INEC na cin rashawa, ya kamata shugaba Buhari ya binciki wannan maganar"

Asali: Legit.ng

Online view pixel