Goodluck Jonathan ya sanya baki cikin rikicin PDP

Goodluck Jonathan ya sanya baki cikin rikicin PDP

-Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yace yana bukatan yin abubuwa da dama domin sulhunta yakin dake kungiyoyin jam’iyyar PDP

-Ya bayyana hakan a lokacin wani ganawa tare da mambobin BoT na jam’iyyar PDP a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja

-Jonathan ya roki mambobin jam’iyyar da su sauke makaman yakinsu domin ci gaban jam’iyyar

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yarda cewa zai shiga cikin rikicin shugabanci dake addaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da niyan kawo karshen rikicin.

Goodluck Jonathan ya sanya baki cikin rikicin PDP
tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan

Yayi Magana a taron Board of Trustees na jam’iyyar karkashin jagorancin shugaban ta Walid Jibrin a babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Laraba 3 ga watan Augusta, Jonathan ya bayyana rikicin a matsayin daya daga cikin kalubalan da ke addabar kungiyar.

Ya ce ya riga ya fara tattaunawa da mutanen da lamarin ya shafa a sirrince kuma ya kamata ya kara kaimi gurin yin haka, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC 700 sun koma PDP

A cewar shi, za’a kawo karshen rikicin cikin karamci. Tsohon shugaban kasar ya nuna danasanin sa kan cewa kotu ta bada umarni kan wanda zai shugabanci jam’iyyar, wanda ya ci gaba da kawowar tabarbarewar lamarin.

Ya bayayana cewa yana sane da abubuwan dake faruwa a jam’iyyar PDP tunda aka fara rikicin. Ya ba da tabbacin cewa kafin taron al’ada na jam’iyyar PDP, duk wani mai ruwa da tsaki a jam’iyyar zasu dawo karkashin jam’iyya daya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel