Cristiano Ronaldo zai sabunta kwantiragin sa

Cristiano Ronaldo zai sabunta kwantiragin sa

– Dan wasa Cristiano Ronaldo zai kare kwallon sa a Kungiyar Real Madrid.

– Cristiano Ronaldo zai sabunta kwantiragin sa da Kungiyar zuwa shekarar 2020.

– Sai dai dan wasan ba zai buga wasan su na Super Cup ba.

Cristiano Ronaldo zai sabunta kwantiragin sa

 

 

 

 

 

 

 

Dan kwallon duniya Cristiano Ronaldo zai kasance da Kungiyar Real Madrid har nan da wasu shekaru hudu

Dan wasa Cristiano Ronaldo na Kasar Portugal zai kare kwallon kafar sa tare da Kungiyar Real Madrid bayan da Kungiyar ta Spain, ta mika ma dan wasan nata sabon kwantiragi har na shekaru hudu. Hakan na nufin dan wasan zai cigaba da taka leda a kulob din har nan da 2020. Tsohon Dan wasan gaban na Manchester United zai cika shekaru 40 cif-cif kenan da haihuwa zuwa lokacin da kwangilar za ta kare, duk kuwa ta kare, a wannan lokaci dole yayi ritaya ya bar ma yara. Jaridar Spanish daily ta Kasar, ta rahoto cewa dan wasan duniyan zai rattaba hannu ne kan wannan sabon kwantiragi muddin ya dawo hutu, suka gana da Shugaban Kungiyar, Florentino Perez a ranar 10 ga watan nan na Agusta.

KU KARANTA: MUHAMMADU SALAH YA KOMA KUNGIYAR AS ROMA

An sayo dan wasa Ronaldo ne daga Man Utd a shekarar 2099, kawo yanzu, ya ci kofunan La-liga, Copa-del-rey, UEFA Champions league, da sauran su, cikin shekaru bakwai. Duk da wadannan, dan wasan na so ya cigaba da zama a Kungiyar ta Real Madrid har zuwa karshen wasan sa. Burin sa shine ya cigaba da wasa a gidan Santiago Bernabeau na Madrid. Ronaldo ya taba bayyanawa cewa, idan har ya wuce shekaru 40, to zai hakura haka, amma dai yanzu abin da ke gaban sa shine, ya dage.

Dan wasan dai ba zai samu buga wasan su na UEFA Super Cup ba, inda za su kara da Kungiyar Sevilla ta gida, kuma yana iya rasa wasannin farko na Gasar La-Liga.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel