Waiwaye: wasu fittatun labarai na ranar Alhamis

Waiwaye: wasu fittatun labarai na ranar Alhamis

Ga bitar wasu fittatun labarai na ranar Alhamis 6 ga watan Agusta 2016

Waiwaye: wasu fittatun labarai na ranar Alhamis

Shekau ya mayar da martani ga nadin sabon shugaba 

‘Yan sa’oi kadan da kungiyar IS ta sanar da nadin Abu Mus’ab al Barnawi a matsayin sabon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau tsohon shugabanta, ya fitar da wani sakon muryarsa, a inda ya ke bayyana yadda ya ke ji game da nadin da kuma matsayinsa.

Kuma : Wata kungiyar yan bindigan Neja Delta sun fasa bututun mai

Kungiyar Tsageru ta Niger Delta Justice Defense Group NDJDG ta kai hari a kan wani bututun mai a Bera da ke karamar hukumar Gokana ta jihar Rivers a safiyar ranar Alhamis 4 ga wata.

Shugaban Boko Haram yayi barazanar kashe dukkan Kiristoci

Sabon shugaban Boko Haram wanda ya IS ta nada,  ya yi hira da wata jaridar Al Naba a inda ya tattauna yakin da kungiyarsa ta Boko Haram ke yi da gwamnati.

Waiwaye: wasu fittatun labarai na ranar Alhamis
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Dr goodluck Ebele Jonathan afadar shugaban kasa a Abuja

Dallin da Goodluck Jonathan ke ziyartar Shugaba Buhari da dare

Shugaba Buhari ya gana da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a fadar Aso Rock da ke Abuja a ranar Laraba 3 ga watan Agusta, ganawar ta su ta kimanin minti 20 ana rade-radin ya karkata ne ga rikicin yankin Niger Delta.

Sarki Sanusi ya jaddada cewa tallafin kudin mai cuta ne

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyan cewa biyan kudin tallafin man fetur wata kafa ce na kara ma masu hannu da shuni karfi da talauta kasa.

 Gasar Olympics: Yan kwallon Najeriya suna nan cirko-cirko a Amerika

Da farko an samu yar matsala wajen shirye-shiryen zuwa Gasar Olympics, na 'yan kungiyar wasan kwallon Najeriya, domin har ta kai Koci  Samson Siaisia na cewa jirgin ‘Character Airline’ sun hana ‘yan Najeriya tashi har sai an biya su kudin su a hannu.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel