Tsohon alkali ya wanke IBB daga zargi kan soke zaben Yuni 12

Tsohon alkali ya wanke IBB daga zargi kan soke zaben Yuni 12

– Dahiru Saleh babban alkalin daya soke zaben Yuni 12, yace Babangida bai tilasta masa ba wajen zartas da hukuncin

– Saleh na mai cewa bashi da nadamar zartar da hukuncin domin bai ga laifin yin haka ba, ya ce in za'a iya maida lokaci baya, abinda zai sake yi ke nan

-Yace Abiola da jam'iyyarsa ta SDP suna da zabin daukaka kara, amma bai san dalilinsu na kin yin haka ba.

Tsohon alkali ya wanke IBB daga zargi kan soke zaben Yuni 12
dahiru saleh mai ritaya

Alkalin da ya soke zaben Yuni,12, 1993 Dahiru Saleh ya wanke tsohon shugaban mulkin soja Ibrahim Badamosi Babangida (IBB) daga zargin soke zaben Yuni 12, 1993 Saleh, a wata hira da mujallar The Interview magazine, ya karyata zargin da ake yi cewa tsohon shugaban mulkin soja IBB ya umurce shi koko ya tilasta masa yin haka

Yace soke zaben yana da nasaba da wadansu shari'u da shi Abiola ke fuskanta wadanda ba'a kammala su ba, ya kara da cewa, in za'a jya maida lokaci baya, hukuncin da zai sake zartaswa ke nan.

KU KARANTA : Sanata Ali Ndume yayi Magana kan abubuwan da suka faru a majalisa

Kan zargin da ake cewa IBB ya tilasta masa zartas da hukuncin, sai yace "tsohon shugaban bai yi haka ba, abin lura shine a wannan lokacin Yarabawa na ma Abiola kallon mai taimakon kowa da kowa saboda haka suna son ya zama shugaban kasa. Allah bai kaddaro ya zama shugaban kasa ba duk da yaso ya zama, ana dora laifin kan shugaba Babangida domin siyasa, amma Babangida bai hana shi zuwa kotuna ba. Duk Wanda bai gamsu da aikina na babban alkali ba yana iya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da kuma kotun koli kuma nayi mamakin rashin daukaka karar"

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel