Dan gaye mai sayar da balango

Dan gaye mai sayar da balango

Wannan abin ya fara zama ruwan dare, dalili kuwa shine, kowa na gogoriyon janyo ma kansa abokan kasuwanci. Ta haka ne yanzu kowa ke kokarin kirkiran sabbin salon neman kasuwa ga kasuwancin sa.

Dan gaye mai sayar da balango

A haka ne aka hangi wani bawan Allah sanye da kayan turawa wato ‘suit’ yana siyar da nama balango, an hangi mahaucin ne sanye da bakar rigar suit da igiyan wuya mai layi layi a unguwar Oluodo yankin Ebute yana siyar ma jama’a nama.

Dan gaye mai sayar da balango

Masu siyan naman nasa sun yabe shi, inda suka ce yana da kirki, kuma baya wasa da sana’arsa. Mu dai anan fatan mu shine kada yayi ta zufa har zufan ya dinga diga cikin naman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel