Maganganu da Abubakar Shekau yayi a bidiyonsa

Maganganu da Abubakar Shekau yayi a bidiyonsa

Bayan sanarwa da ISIS tayi na cewa ta zabi sabon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram da ake  tunanin an kashe a lokuta da dama, “ya dawo” cikin wani bidiyo yana karyata rahoto na cewa bas hi bane shugaban yan ta’addan Boko Haram a yanzu.

Maganganu da Abubakar Shekau yayi a bidiyonsa
 Abubakar Shekau

Mu tuna cewa Shekau yayi matsayin mataimakin shugaban wanda ya asassa kungiyar, Mohammed Yusuf, kuma mahaifi ga Abu Musab al-Barnawi, har sai da aka kashe Yusuf a shekara ta 2009.

Hukumomin yan Najeriya sun yarda cewa an kashe Shekau a shekara ta 2009 a lokacin wani karo tsakanin jami’an tsaro da yan Boko Haram har watan Yuli na shekara 2010, lokacin da Shekau ya bayyana a wani bidiyo yana bayyana cewa shine shugaban kungiyar. An rahoto cewa ya mutu a lokuta da dama.

KU KARANTA KUMA: Bamu tsorata ba- Avengers Aisha Musa 29 minutes ago 47

Ga abubuwan da ya fada a bidiyonsa

1.Har yanzu Shekau ne shugaban kungiyar in Allah ya yarda.

2.Mutane su dauki wannan sakon da muhimmanci domin zai amfaneku dukka.

3.Abu Musa Al Barnawi yace wasu Musulmai sun zama kafirai. Dukkan wanda muke gani a matsayin kafiri toh kafiri ne saboda mu mun yarda da Allah; dukkan abunda mukeyi yana cikin Qur’ani da littafin annabi Mummadu kuma dole mu yada sako; bazai yihu ka zama musulmi kuma ka zama kafiri a lokaci guda ba; ku mutanen duniya kun san haka amma kuke yi kamar baku sani ba.

4.Mutanen duniya basu da zabin da ya wuce su sauraremu kamar yanda muke bin abunda littafin Allah yace.

5.Wannan sako ya fito daga shugaban Musulmai mai suna Abubakar Al Baghdadee Abu Musa Al Barnawee, cewa dukkan abunda ku mutane kuke bi karya ne, haka kuma kuna bin sahun wadanda basu kan hanya madaidaiciya, dukkan abunda kuke fada wa mutane maganganu ne na shirka da kafirci.

6.Naji dukkan abunda ake fada. Yace shi ne Abu Muhammad bin Muhammad Shekau.

7.Naji dukkan abunda aka ce da Larabci cewa babu shugaba wanda nake so na karyata

8.Dukkan abunda ake fada a gidajen radiyo a duniya abubuwane da bamu sani ba.

9.Dukkan abunda aka rubuta ba haka yake ba.

10.Dole na fada ban mutu ba kamar yanda a yanzu ina kasar Kafirai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel