Auren Jaideep Jadhav da Reshma Patil a sararin samaniya

Auren Jaideep Jadhav da Reshma Patil a sararin samaniya

An daura auren Fitaccen fasihi Jaideep Jadhav da amaryarsa Reshma Patil a wani biki da ya baiwa kowa mamaki a yammacin yankin Ghatsa na kasar Indiya.

Auren Jaideep Jadhav da Reshma Patil a sararin samaniya

Don son nuna muhimmancin yawon bude ido, ma’auratan sun yanke shawarar zama abin koyi ga na baya inji shugaban masu wasa kan manyan duwatsu na Kolhapur Vinod Kamboj da ya shirya auren.

Auren na Jaideep Jadhav da Reshma Patil an daura shine a tsakiyan sararin samaniya a tsakanin manyan duwatsu biyu da tsawon kowanne a cikinsu ya kai kafa 3000, wato dutsen Vishalgadh da Panhala, kusan kilomita 15 a saman kauyen Bhattali.

Auren Jaideep Jadhav da Reshma Patil a sararin samaniya

mu ko daga nan muna taya ma’auratan murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel