Ba ni barin Kungiyar Chelsea-John Mikel Obi

Ba ni barin Kungiyar Chelsea-John Mikel Obi

 

– Dan wasa Mikel Obi yace fa yana nan a Chelsea ‘Da-ram-dam-dam’!

– Kyaftin din na Super Eagles yana san ran a kara masa kwantiragin sa.

– …Duk da dai zai yi wahala ya samu wuri a Kungiyar.

Ba ni barin Kungiyar Chelsea-John Mikel Obi

 

 

 

 

 

 

Kyaftin din Kungiyar Super Eagles Mikel Obi John ya karyata rade-radin cewa zai bar kulob din, ya koma Kasar China. Dan wasa Mikel Obi yace zai tsaya a Kungiyar yana nemi wurin sa. Kyaftin din na Najeriya yake cewa: “Ina so in ga na taimaki Kungiya ta, ina son cin kofuna, kuma ina son ganin mun koma Gasar Champions league da wuri” Mikel John Obi yake ce ma Jaridar Evening Standard: “Shekaru gome kenan ina nan, ba abin da ya canza, ina wannan babban Kulob, mai kungiyar mutumin kirki ne, mun zama tamkar ‘yan uwa, kamar jinni da hanta…” Ganin ya shafe shekaru goma cur a kulob din, kuma saura masa shekara guda rak a kwantiragin sa, Dan wasan yana ganin cewa idan har ya dage karkashin sabon Kocin Kungiyar, Antonio Conte, zai samu a kara masa kwangilar sa. Mikel yayi alkawarin yin iya bakin kokarin sa a cikin fili don ganin an sabunta kwantiragin na sa.

KU KARANTA: MIKEL OBI NA CHELSEA YA SAKE SUNA

Mikel Obi ya nuna godiyar sa ga Kungiyar ta Chelsea da ta kyale sa ya tafi Gasar Olympics, har Kocin Kungiyar yace da shi ya dawo da kyautar ‘gwal’. Dan wasan ya bayyana cewa, ya nemi alfamar Kungiyar, kuma ya dace aka basa damar zuwa Gasar Olympics, ya kuma godewa Kungiyar dalilin haka, har Kocin yayi masa fatan alheri. Dan wasa Mikel Obi mai shekaru 29 yana ganin cewa zai fuskanci barazana wajen buga ma Chelsea a kai-a kai, ganin akwai yan wasa irin su N’golo Kante, Cesc Fabregas da Nemanja Matic. Sai dai dan wasan na tsakiya yace zai yi kokarin burge Kocin har ya samu bugawa bisa kari.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel