Hukumar sojan Najeriya ta mayar da martani ga sabon shugaban Bokoharam

Hukumar sojan Najeriya ta mayar da martani ga sabon shugaban Bokoharam

Hukumar sojan kasar nan ta mayar da martani biyo bayan nadin da kungiyar ISIS tayi ma Abu Mus’ab Albarnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar Bokoharam.

Hukumar sojan Najeriya ta mayar da martani ga sabon shugaban Bokoharam
Mus'ab Albarnawi

Rundunar sojan tace ko dar bata ji ba dangane da nadin Albarnawi, wannan ba wani abin damuwa bane, asali ma haka hakan na nuni da cewa sun gama da kungiyar Bokoharam ne.

Daraktan watsa labarai na hukumar soja Birgediya Rabe Abubakar yace hukumar soja bata damu da duk abin da ke faruwa a cikin kungiyar Bokoharam ba, don haka babu wani abin damuwa idan Bokoharam tayi sabon shugaba ko kuma ta kulla alaka da ISIS.

Birgediya Rabe yace abin da ke gaban hukumar soja shine ta gama aikin rugurguza kungiyar Bokoharam ba tare da la’akari da koma wanene shugabanta ba. Yace “zancen nadin sabon shugaban Bokoharam bai razana mu ba ko yaya, saboda kungiyar na gab da mutuwa gaba daya a kasar nan da kuma a makwabtanta. Don haka ko sun yi sabon shugaba ko babu, wannan ba damuwar mu bane, abin da muke da tabbas akai shine, zamu karar da yan kungiyar Bokoharam. “niyyar mu shine mu fitar da yan bokoharam daga maboyarsu, kuma shine abin da muke yi ta hanyar sabon shirin da muka fara mai suna Operation gama aiki tare da rundunr sojojin hadin kai na kasashen afirka. Fatan mu shine mu cigaba da karya lagonsu”

Abubakar ya cigaba da cewa “haryanzu muna ta kama yan ta’addan, don haka canjin shugabancin su ba wani abu bane a wurin mu.” Yace hukumar Soja na sane da cewa kungiyar Bokoharam ta shiga rudani kuma suna rugujewa. Don haka ne suka zama kamar mutumin da zai nutse cikin ruwa, ko wuka ka mika masa zai kama. Kada jama’a su dauke zancen su da muhimmanci, don basu iya yin wani barazana ga al’umma, don haka mun dauki zancen canjin shugabans cin su a matsayin wasan yara ne kawai” in ji shi.

An ruwaito cewa an ga sabon shugaban Bokoharam Albarnawi a cikin jaridar ISIS, inda kuma ba’a ambaci sunan shekau ba. A ranar Laraba ne kungiyar yan ta’adda ta ISIS ta sanar da nadin sabon shugaban Bokoharam Mus’ab Albarnawi don maye gurbin Abubakar Shekau wanda a baya shine mai magana da yawun kungiyar.

ISIS ta bayyana sunan sabon shugaban, amma bata yi bayani ba akan Shekau wanda tun watan agusta na 2015 ba’a sake jin duriyarsa ba. Su ko sojoji sun ce sun samu nasarar cafke wasu gaggagaggan yan kungiyar ta Bokoharam Mohammed Mohammed Zauro a sabon garin karamar hukumar Damboa, jihar Borno. A cewar sojojin, sun kama mutumin ne da misalign karfe 8:30 na safiyar litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel