An kunyata yarinyan James Ibori a wajen Jana’iza

An kunyata yarinyan James Ibori a wajen Jana’iza

An kunyata yarinyar wannan tsohon barawon gwaman nan James Ibori a wata taron jana’iza da akayi .

Saboda kasancewan mahaifinta baya nan yana gidan yari a kasar ingila, Erhiatake Ibori ta wakilce shi a wajen taron domin ta karanta takardan jana’iza a taron jana’izan da akayi domin girmama Olorogun Felix Ibru.

An kunyata yarinyan James Ibori a wajen Jana’iza
Erhiatake Ibori

Erhiatake Ibori , wata yar majalisan dokokin jiha mai wakiltar mazaban Ethiope a jihar delta , ya kunyata ta akan mimbari kafin ta gama karanta abinda tace a karanta da akayi a gidan gwamnatin jihar delta da ke Asaba.

Game da jaridar sahara reporters, Erhiataketa nuna rashin kwarewa tun lokacin da ta hau mimbari domin gabatar da Magana. Yar majalisan dokokin yar shekaru 36 ta kasa karanta takardan da aka bata. An bada rahoton cewa tana a firgice ta kasa furta wasu kalaman turanci

Ayarin mutanen da ke wurin suka fara yi mata iwu a wurin taron yayinda ta cigaba da yin kuskure wajen karanta sakon har sai sanda tsohon gwamnan jihar Emmanuel uduaghan , wanda ya gabatar da nasa sakon da kwarewa ,har dan bada dariya a wajen.

KU KARANTA : Rundunar Soja ta kama barayin shanu a Zamfara

Uduaghan yace la’alla gilashin Erhiatake ne ke da matsala , hakan yasa mutane suka fashe da dariya har suka manta da abinda ya faru

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel