Rundunar Soja ta kama barayin shanu a Zamfara

Rundunar Soja ta kama barayin shanu a Zamfara

Rundunar sojojin Najeriya ta cafke wasu barayin shanu a dazuka daban daban na jihar Zamfara. An samu wannan nasarar ne a ranar Litinin 1 ga watan agusta na shekarar 2016.

Haka zalika a ranar ne rundunar soja ta watsa gungun yan bokoharam da suka yi yunkunrin kai hari a garin Yauri na jihar Borno. Jami’i mai magana da yawun rundunar soja kanal Sani Kuka sheka yace runduna ta daya ne ta kai farmakin a lungunan da yan fashin ke buya a cikin dazukan.

Wasu daga cikin barayin da aka kama

Rundunar Soja ta kama barayin shanu a Zamfara
Rundunar Soja ta kama barayin shanu a Zamfara

 

Rundunar Soja ta kama barayin shanu a Zamfara

“rundunar sojojin ta kai harin ne yankin dazukan Batara da Ajah a yankin Birnin Magaji da karamar hukumar Gusau na jihar Zamfara.

“duk da cewa yan fashin sun tsere daga shingayensu, rundunar ta lalata shingayen nasu, kuma ta kwato Babura guda uku da wayoyin salula guda biyu. Sa’annan sun kai samame a dajin Rimawa na karamar hukumar Gusau inda suka kama barayi guda biyu da ake neman ruwa a jallo, Aliyu Abubakar da Umar Ibrahim.

“haka nan ma rundunar sun kama wani kasurgumin dan fashi a dajin Bini dake karamar hukumar Maru, mai suna Umar Dan Bilbili,” in ji kanal Usman. A harin da aka kai a jihar Borno, rundunar sojan kasa sunce jami’an su sun hada kai da yan kato da gora inda suka kai wani samame suka kashe yan ta’adda biyar, kuma sun kwato makamai da alburusai da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel