Jonathan ya kawo ziyara fadar Shugaban Kasa

Jonathan ya kawo ziyara fadar Shugaban Kasa

A yau ne, 3 ga watan Agusta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kawo ma shugaban kasa Muhammadu Buhari  ziyara fadar shugaban kasa .

Mai daukan hoton shugaban kasa , Bayo Omoboriowo ne ya watsa a shafin sada zumuntansa ta instagram, yace an yi ganawar ne a sirrance. Jonathan ya iso fadar shugaban kasa ne a  wata mota Range Rover marked KWL 86 CN  kuma daya daga cikin ma’aikatan Buhari ne ya tarbe sa .

Jonathan ya kawo ziyara fadar Shugaban Kasa

Labarai sun fara fitowa akan makasudin ziyarar da tsohon shugaba Jonathan ya kawo ma buhari ; gas su nan

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya zo tofa albarkacin bakinsa akan hayaniyar da ke faruwa a yankin Neja Delta da kuma yadda abubuwan da ke faruwa na fashe-fashen bututun mai da ke durkusar da tattalin arzikin kasa.

Kungiyar tsagerun neja delta sun durkusar da tattalin arzikin Najeriya

Karkashin jagorancin shugaba jonathan,Tattalin arzikin kasan najeriya tanada armashi fiye da yadda take karkashin Gwamnatin Buhari.

Abinda shugaba Buhari yayi amfani da shi wajen yakin neman zabe shine cewan zai yi yaki da rashawa . kuma bayan ya lashe zaben ,ya damke abokan aikin Jonathan da dama.

KU KARANTA : Ya mutum bayan hawa palwayan wuta a taron siyasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel