Zaman Abdulmumini Jibrin da Shugabannin APC

Zaman Abdulmumini Jibrin da Shugabannin APC

–Shugabannin jam’iyyar APC tace jam’iiya bata da hurumin yanke hukunci akan al’amarin aragizon kasafin kudin shekaran 2016.

–Jam’iyyar ta musanta cewa tana shirin sanya ma Abdulmumni  Jibrin takunkumi akan maganganun da yakeyi a kafafun yada labarai da shafin sadar da zumunta akan kakakin majalisa Yakubu Dogara.

–Jam’iyyar tace bata sa baki ko sulhu tsakanin mutanen biyu

Game da kasafin kudin kasa da ke faruwa a majalisan wakilan tarayya , shugabannin jam’iyyar APC a ranar talat ,2 ga watan agusta sun hadu da tsohon shugaban kwamitin majalisan wakilai, Abdulmumini Jibrin , a sakatariyan jam’iyyar a birnin tarayya ,Abuja.

Zaman Abdulmumini Jibrin da Shugabannin APC
abdulmumini jibrin a hanya

Jam’iyyar ta ce ta tura goron gayyata ga saboda jibrin yaki yarda a kira shi a wayan sadarwa. Jibrin yace baza’a same shi a way aba saboda ya lura da cewan dogara na shirin yin garkuwa da shi.

Ya gana da mataimakin shugabanjam’iyyar ta kasa na arewa, Lawal Shuaibu; sakataren kasa ta jam’iyyar , Mala Buni; da mataimakin shugaban jam’iyyar ta yankin arewa maso yamma, Inuwa AbdulKadir. Shuaibu yace jam’iyyar ta riga tayi magan da kakakin majalisan,yakubu dogara, tace jam’iiayr bata da hurumin yanke hukunci akan aragizon kasafin kudin .

Mataimakin shugaban jam’iyyar ta kasa, yankin arewa,ya musanta cewa jam’iyyar na shirin sanya wa Abdulmumini jibri takunkunmi saboda maganganun da yakeyi a kafafun yada labarai. Yace jam’iyyar zata cigaba da Magana da Jibrin da Dogara ,amma bata sulhu da sub a har yanzu.

KU KARANTA :Waiwaye: Wasu fittatun labaru na ranar Talata

A wata labari kuma, jibrin yace ba kwamitin ladabtarwa ce ta gayyace shi ba amma kawai jam’iyya ce ta gayyace shi akan hayaniyar aragizon kasfin kudin kasa da akayi a majalisan wakilai ta kasa.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel