Sabuwar rigar Kungiyar Super Eagles (Cikin Hotuna)

Sabuwar rigar Kungiyar Super Eagles (Cikin Hotuna)

 

– Yan Kungiyar kwallon Super Eagles ta Najeriya za su sanya sabuwar riga.

– Kamfanin NIKE su ka zana sabuwar rigar kwallon na Super Eagles.

– An yi amfani da fasahar Dri-FIT wajen dinka wannan riga.

Sabuwar rigar Kungiyar Super Eagles (Cikin Hotuna)

 

 

 

 

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya (Watau NFF) ta sanar da cewa Kungiyar kwallon kafar Kasar (Super Eagles) tayi sabuwar rigar kwallo, Hukumar ta NFF ta nuna sababbin rigunan da Super Eagles har guda biyu; ana sanya daya ne idan ana wasa a gida Najeriya, daya kuma idan an bar Kasar. Rigar gidan ta ce koriya shar, fara kuma sai an fita gida, farar rigar tana da wani dan ‘kwala’ matashin wuya na zamani a jikin ta. An dai yi amfani da fasahar Dri-FIT wajen dinka wannan riguna. Kuma, Kamfanin NIKE ne ta zana ta.

KU KARANTA: Get the latest sports news on Naij Sports App

Hukumar kwallon Kafar Najeriya, NFF ta bayyana cewa sabuwar rigar ta hana gumi a jiki, fasahar Dri-FIT da NIKE suka yi amfani da shi ya sanya rigar ba ta barin zufa ko kadan, daga gumi ya keto, sai tayi kasa da shi yayi waje, inda zai bi iska. Hakan zai taimaka wajen sa ‘yan wasan su dage, su zage su yi kwallo ba tare da wata matsala ba. Duk a jikin wannan riga dai, akwai wasu kananan huji da ramuka da za su sanya iska ya rika ratsa dan wasa ta ciki, akwai wani faifan faranti da ke hana sanyi ko zafi yayi wa mutum yawa duk a jikin wannan riga.

An dai dinka rigar ne da wani irin samfurin yadi na dabam, a gaba da baya akwai wasu abubuwa jikin rigar da ke sanya iska ta rika shiga ciki, tana yawo. Hakan zai yi kokarin taimakawa dan wasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel