Wani Mutum ya yanke hannun  Matarsa hannu

 Wani Mutum ya yanke hannun Matarsa hannu

Wani mutum dan shekara 34 mazaunin kasar Kenya mai suna Stephen Ngila Thenge an bayyana cewar ya yanke ma matarsa hannaye wace suka kwashe shekaru bakwai dayin aure batare da sun Sami haihuwa ba.

Acewar jaridar Popular Daily dake Kenya, mijin matar dai mai suna Stephen ya yanke ma matarsa mai suna Jakline Mwende dake kyauyen Kathama a Majii dake Machakos County hannayen ta, kuma tun daga wuyan hannun ta.

 Wani Mutum ya yanke hannun  Matarsa hannu

Haka kuma ta samu raunika a kanta dakuma wuyan ta sakamakon kokuwar da sukayi dashi. Wani dan uwansu ya bayyana cewar damar ma'auratan suna samun matsala wanda harya kaiga ita Ms Mwende taso ta rabu da mijin nata amman Faston su yayi mata nasiha datayi hakuri domin kuwa abunda take shirin yi toba abu mai kyau bane.

Da take bayyana yadda abun ya faru a gidan mahaifinta, wanda anan ne takeyin jinya bayan da aka sallameta daga asibiti a ranar juma'a, 29 ga watan yuli, Ms Mwende a gidan mahaifin nata dai wato Kathama tace, kafin abun ya faru daman sun rabu da mijin nata na tsawon wata uku, sakamakon rashin haihuwa da basu samu ba.

KU KARANTA : Manyan abubuwan da ke faruwa a Najeriya

Ta kara dacewa " ban gane mai yake nufi ba, saboda kuwa munje asibiti a shekarar daya wuce, likita ya dubamu inda yace matsalar a wajen shi take, inda likitan yace masa zai bashi shawaran magungunan daya kamata yayi amfani dasu, inda yaki bin shawarar likita akan maganin, wanndan daga nan yabar gidan na tsawon wata uku sannan ya dawo ranar lahadi 24 ga watan yuli da misalin karfe 8:30 na dare, dana Bude masa kofar dakin kawai sainaji yace min wai yaune ranata ta karshe, a inda ya fara yankar Naman jikina da wata katuwar wuka".

A lokacin datayi ihu domin azo a ceceta, sai ya gudu kafin makotansu suzo su kaita asibiti.

Wannan Tsabar jahilcine gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel