An kama mutane 2 domin satan wayoyin wuta a Legas

An kama mutane 2 domin satan wayoyin wuta a Legas

–An kama wasu mutane biyu ta dalilin satan wayoyin wutan wani kamfani  a Legas

–Kakakin kamfanin ya bayyana yadda aka kama su

Jami’an tsaro sun kama wasu mazaje biyu ta dalilin satan wayoyin wuta na kamfanin Eko Electricity Distribution Company (EEDC), da ke Apapa a Jihar Legas. An samu cewa an kama su biyun ne saboda ana sani cewa suna daga cikin wasu kwarrarun barayin wayoyin wuta 12 masu satan wayoyin wutan mutane a unguwa.

An kama mutane 2 domin satan wayoyin wuta a Legas

Game da cewar Jaridar Daily Trust, shugaban sadarwa na kamfanin EEDC , Godwin Idemudia ya bayanna cewa barayin sun yi rashin sa’a ne yayinda suke shirin loda waya mai mita 12 cikin motan su. Yace wayoyin wutan da suka sace na daga Vanilla 11kv da ke daukan caji daga ofishin Apapa

Jami’an tsaron kamfanin A-Z petroleum ne suka damke su kuma am kaisu ofishin yan sanda da ke Ebute Meta.

A wata labara mai kama da hakka, an kama wani direba da satan motan kamfani, ko kwana daya bai cika da fara aiki a kanfanin ba.

KU KARANTA : EFCC ta kai farmaki ofishin filin jirgin sama a Legas

Game da rahotanni,an kama  direban dan shekaru 30 mai suna jimoh taoreed a garin Ibadan, birnin Jihar Oyo.  Jimoh, wanda aka dauka domin ya dinga sayar musu da ruwan leda ya yaudari yaron da aka sa ya dinga tayashi ,yace masa ya jira shi zai je ya ciro kudi a banki a unguwar bodija. Sai ya bar yaron kawai ya arce da motan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel