Manajan Banki ya kashe kansa kan bashin naira miliyan 350

Manajan Banki ya kashe kansa kan bashin naira miliyan 350

Rahotanni suna nuna cewa wani ma’aikacin banki dake Legas mai suna Olisa Nwakobe ya kashe kansa kan maganan bashi a wurin aikin sa.

Manajan Banki ya kashe kansa kan bashin naira miliyan 350

Olisa ma’aikaci kuma manaja a bankin FCMB ya bindige kansa har lahira a gaban faston cocin su a ranar jum’a 29 ga watan yulio bayan ya bayyana ma faston nasa da ya fada ma matarsa da ta kula da yaransu. Olisa dan marigayi Cif Patrick Oguejiofor Nwakobi ya dauki ransa ne bayan an hura masa wuta da ya biya bashin naira miliyan 350 da ya bai wa wani mutum.

Olisa ya fara tunanin hakan zai bata mi shi suna kuma cin mutunci ne a wurinsa idan bankin suka yanke shawarar korar sa daga aiki a dalilin bashin. Baban Olisa ya taba zama babban lauya, dan siyasa kuma babban mutum mai mutunci a tsakanin al’ummar iyamurai na garin Nkwelle Ezunaka dake jihar Anambra. Jami’an tsaro na Area J dake Ajah/Lekki suna kan binciken lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel