Jigo a MASSOB ya ce Najeriya ta cancanci rabuwa

Jigo a MASSOB ya ce Najeriya ta cancanci rabuwa

-Kungiyar 'yan rajin Biafra, (MASSOB) na daya daga cikin kungiyoyin neman 'yancin mutanen kudu masa gabas

– Sunday Chukwu, na cewa korafe-korafen jama'a a cikin kasar ya zama sheda cewa kasar ta cancanci rabuwa

-Yana tunanin ko kasar ta shirya ma wani yakin basasa kafin  rabuwa, ya jaddada cewa lallai a tattauna zamantakewar kasar.

Jigo a MASSOB ya ce Najeriya ta cancanci rabuwa
Mambobin massob

Wani jigon kungiyar (MASSOB) na kasa Chief Solomon Ordu Chukwu, yace matsalolin da ke addabar Najeriya sun Isa su tarwatsa kasar. Jaridar The Sun ta ruwaito shugaban na fadin haka ta yawun daraktan watsa labarai na kungiyar Sunday Okereafor, Chukwu, yana cewa korafe-korafen sun Isa su raba kasar.

KU KARANTA : Nnamdi Kanu ya ce Allah ne ya yanke hukuncin neman Biyafara

Ya ci gaba da cewa, "yanzu a cikin kasar akwai 'yan ta'addan Boko Haram a arewa maso gabas wadanda basa son ilimin boko, amma suna son kowa ya zama musulmi, suna kisa da barna a wannan yankin. Haka kuma Fulani makiyaya, suna barazana ga kasar baki daya. Suna kisa, satar mutane, fyade da lalata amfanin gona ba tare da gwamnati tayi wani abu ba. A yankin Neja Delta, ga 'yan Neja Delta Avengers (NDA) wadanda kamar danginsu watau (MEND) suna kokarin gurgunta tattalin arzikin kasar. A kudu maso gabashin kasar ga MASSOB wadda ke nata gwagwarmayar ba tare da tashin hankali ba. Da wadannan matsalolin, ya'ya za'a ce ba za'a tattauna zamantakewar kasar ba?."

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel