Wani dan shekara 4 kacal amma mai siffar tsaffi (Hotuna ciki)

Wani dan shekara 4 kacal amma mai siffar tsaffi (Hotuna ciki)

Wannan yaro nan dan shekara 4 kacal a duniya amma bazaka taba cewa haka ba idan ka ganshi saboda irin siffar tsaffin da ke gare shi.

Shi dai wannan 'yaron' dan kasar Bangladesh ne kuma sunan sa Bayezid Hossain. A fuska ma zaka iya cewa ya girmi mahaifiyarsa. Ance yana dauke ne da wata cuta ma sa tsufa da wuri wadda ake kira progeria. Cutar wadda ba'a cika samun ta ba ance tana sa kasusuwan masu ita suyi rauni sannan kuma ganin su ma ya rage kai hatta hakoran su ma sai su fara zubewa.

Wani abun mamaki kuma shine mahaifin yaron ma kanshi shekarar sa 22 wannan ne ma yasa a fuska yaron ya girmi mahaifin sa nesa ba kusa ba. Uwar tasa tace tun yana da watanni 3 ya gama fidda hakoran sa dukka. Yanzu haka ma dai yana so ya fita yaje wasa tare da sauran yara amma tsufa ya hana.

Wani karin takaici kuma yanzu shine yadda mutanen kauyen su suke gudun su suna cewa wai fushin ubangiji ne a kan su da ma dai sauran yan camfe-camfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel