Wayyo! A bayyana kudurorin Keshi kafin mutuwar sa 

Wayyo! A bayyana kudurorin Keshi kafin mutuwar sa 

Tsohon mataimakin mai horarwa Stephen Keshi Valere Hounandinou ya bayyana kudurorin da mamacin Keshi yake da su kafin mutuwar sa.

Shi dai mamacin wanda kuma shine tsohon jagoran kungiyar Super Eagles Stephen Keshi ya mutu ne a ranar 8 ga watan Juni bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya.

Wayyo! A bayyana kudurorin Keshi kafin mutuwar sa 

Kafin mutuwar sa dai shine ya jagoranci kungiyar kwallon kafar Najeriya watau Super Eagles ya zuwa lashe gasar cin kofin kasashen Afrika wanda akayi a kasar Afrika ta kudu wanda hakan ne ma ya maida da mutum daya tilo da ya taba lashe gasar a matsayin dan wasa da kuma mai horarwa.

An dai rufe Keshi din a kauyen sa dake Ukpologwu Illah a jihar Delta.

A wata kebantacciyar fira da tsohon mataimakin nasa yayi da gidan jaridar Legit.ng sashen wasanni, Hounandinou ya bayyana cewa aminantakar shi da mamacin ta soma ne tun a shekara ta 1979 a lokacin da suka buga wata gasa a kungiyar su ta ACB FC a garin Legas.

Da yake bayyana kudurorin mamacin kuma, Hounandinou ya ce Keshi din yana da kudurin wallafa littafi kan rayuwar sa da kuma fadi-tashin sa a bangaren wasanni dama horarwa sannan kuma har ilayau yace mamacin yana da kudurin bude makarantar koyon kwallon kafa irin na kasashen turai.

Source: Legit

Online view pixel