Yan Najeriya sun yi kaca-kaca da Shugaban NFF

Yan Najeriya sun yi kaca-kaca da Shugaban NFF

 

– Shugaban NFF, Pinnick bai hallarci taron birne Keshi ba da aka yi a Garin Illah na Jihar Delta.

– Mutanen Kasar Najeriya wannan abu bai masu dadi ba sam.

– Amaju Pinnick na NFF din ya bayyana cewa rashin lafiya ya hana halarta tun da farko.

Yan Najeriya sun yi kaca-kaca da Shugaban NFF

 

 

 

 

Mutanen Najeriya sun yi kaca-kaca da Shugaban NFF, Amaju Pinnick saboda rashin hallartar jana’izar Marigayi Kocin Najeriya, Stephen Keshi. An rufe Stephen Keshi ne a ranar Jumu’ar nan a Garin Illah da ke Jihar Delta. Pinnick dai ya hallarci duk taron bikin mutuwar Marigayin, sai dai bai samu zuwa ranar da aka bizne tsohon Kocin Kasar cikin kasa ba, ya bada uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin da ya sa bai samu hallarta ba. Shugaban na NFF ya sha suka dangane da rashin hallartarntar taron wannan ranar. Ga wasu daga cikin abin da yan kasar ke cewa game da Shugaban na NFF, Amaju Pinnck bayan da ya rasa hallartar taron rufe Keshi.

KU KARANTA: KWANA SUN KARE, KOCI KESHI YA RIGA MU GIDAN GAASKIYA.

Kyaun ta a jefe AMAJU Pinnick kawai, ba shi da dalilin rasa jana’izar Keshi.

Duk sun yi ki zuwa wajen rufe Keshi, sai kace su ba za su mutu ba wata rana. Wai har da Pinnck, wanda ya kamata ace shine na farko. Tir!

Shi dai Shugaban Hukumar ta NFF ya bayyana cewa, duk wani taro da aka gudanar, da shi aka yi. Ranar karshe ne kurum bai samu hallarta ba dalilin rashin lafiya da ya kama sa. Pinnick yace akwai takaci ganin yadda mutane ke suka bayan ba su san cikakken abin da ya wakana ba. Pinnick yace da shi aka je Garin Benin inda aka yi addu’a, daga nan suka tafi filin wasa har aka gama taro, haka kuma Amaju Pinnick yah au mota har Garin Asaba inda har ya gana da iyalan mamacin. Daga nan ne washegari larura ta kama sa bayan da har ya fara tafiya, da abin ya faskara ne ya aika wani jami’i daga Garin Fatakwal domin ya wakilce sa, kuma hakan aka yi.

An dai birne Marigayi tsohon Kocin Najeriya, Stephen Keshi ne a ranar Jumu’ar nan a Garin Illah da ke Jihar Delta.

 

Source: Legit Newspaper

Online view pixel