Rashawa:Buhari zai kore ne in ina da laifi - Amaechi

Rashawa:Buhari zai kore ne in ina da laifi - Amaechi

-Amaechi na alfahari ba cin rashawa lokacin mulkin sa

-Ya kalubalanci duk mai shedar cin rashawa game dashi ya kawo domin a tuhumceshi

-Ya bayyana yadda wasu ministoci suke tsugunne a Abuja mamadin zaton da ake cewa suna Aljannah duniya

-Ya ki cewa uffan game da shiryawa da gwamna Wike

Rashawa:Buhari zai kore ne in ina da laifi - Amaechi

Chibuike Rotimi Amaechi, ministan sufuri ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai koreshi in aka kama shi da laifin cin rashawa Tsohon gwamnan jihar Rivers na mai cewa (ba kamar yadda ake tunani ba) wasu ministocin rakube suke a Abuja kamar sauran 'yan Najeriya

A wata hira da yayi da Osasu Igbinedion a filinsa na Osasu Show, ministan wanda ake yabo saboda kammala aikin jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna yace "sauraranni, shin kana sane cewa a halin yanzu ministoci rakube suke a Abuja? Rayuwarmu irin ta sauran 'yan Najeriya ce".

KU KARANTA : Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben Jihar Imo

A cewar jaridar The Cable, Amaechi yaci ga a da cewa "Wadanda basu da gidaje, sai su kama hayar gidaje masu sauki a Kaduna mamadin Abuja. Zaka samu rarar kudi a hannun ka. Zai yi tasiri ga noma da amfanin gona ya kuma rage kudin aikace-aikace domin ka sami saukin sufuri"

Asali: Legit.ng

Online view pixel