Sojoji da yan banga sun samu sabani

Sojoji da yan banga sun samu sabani

Sojoji sun lallasa wasu yan banga a karamar Hukumar Igboeze ta arewa  a Jihar Enugu.

- Wasu yan bangan sun tare hanyoyi sun hana sojojin wucewa.

- DPO na karamar Hukumar igboeze ta arewa  yace wani soja ya kawo karan zancen ofishinsu cewa an kwace wasu kayan da aka turo masa daga kasan waje.

Sojoji da yan banga sun samu sabani

Har ila yau akwai tashin hankali a karamar Hukumar Igboeze ta Arewa  yayinda Sojoji suka far ma wani ofishin yan banga domin kwato kayayyakin da wasu yan banga suka kwace a hannun abokinsu. Game da cewar Jaridar Vanguard, sojojin sun zo misalin karfe 2 na rana suka lallasa ya bangan sannan suka kwace makaman su  suka bata wurare a ofishin su. Jin haushin haka, wasu yan bangan suka tare hanyar da yan bangan zasu wuce .

DPO na yan sanda ya sanar da shugabannin sa da ke enugu akan aninda ke faruwa. Yayinda ya ke magana ,wani dan sanda da ke ofishin yan sanda a nsukka yace anyi iyakan kokari domin bude hanya ga sojoji su wuce ,su kuma akai matsalar ofishin yan sanda domin a warware.

KU KARANTA : Akwai danyen mai a Yankin Bidda – Gwmanatin Neja

 “Da mun tafi ofishin yan sandan ogurute, amma muna jiran mai gyaran taya ne ya samana iska a tayan bayan motan sojojin domin ta sace. Dan sandan yace.

A bangare guda, rundunar sojin najeriya ta ce za'a  fara hada makamai a najeriya, kwamanda kwalejin tsaro , rear admiral samuel alade ne ya bayyana haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel