Iheanacho yana buga kwallo karkashin Guardiolo 

Iheanacho yana buga kwallo karkashin Guardiolo 

Shahararren matashin dan kwallon kasar Najeriya kuma dan kulob din Man city Kelechi Iheanacho yana cikin tawagar yan wasan da suka lallasa kungiyar Borussia Dortmund a wani wasan share fage da suka buga a China.

Iheanacho yana buga kwallo karkashin Guardiolo 
Kelechi Iheanacho

Dan wasan Man city Aguero ne dai ya fara jefa kwallo a wasan a minti na 79 kafin daga bisani Christian Pulisic ya rama ma Dortmund din minuta 6 kacal bayan Aguero. Wannan nema ya sa aka buga bugun-daga-kai-sai-mai tsaron gida wanda kuma Man city din ta lashe da ci 6 - 5.

Mai horar da kungiyar ta Man city Pep Guadiola dai ya bayyana cewar akwai bukatar suyi yan gyare-gyare nan-da-can kafin kankamar kakar wasannin mai zuwa. Yace: "Bana so in yi korafi akan yadda muke wasa amma dai ina so mu kara kwazo a fannonin mu da dama".

Shi dai dan wasan na Najeriya iheanacho ya zubda wata dama da ya samu a sashen farko na wasan kafin zuwa hutun rabin lokaci. Kawo yanzu dai Guardiola yana cigaba da nuna sha'awar sa ta ganin ya siyo karin yan wasa 2 da suka hada da John Stones da kuma Leroy Sane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel