Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade 5

Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade 5

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yau Juma'a 29 ga watan Yuli yayi sabbin nade-nade har guda 5 na ma'aikatu daban daban a fadin kasar.

Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade 5

Mataimakin shugaba Buhari akan harkokin watsa labarai Bashir Ahmad ya sanar da hakan ga manema labarai. A cikin sanarwar Bashir Ahmad din ya sanar ta hanyar asusun sa na shafin kafar zumuntar zamani na Tuwita cewar Shugaba Buhari ya amince da nade-naden shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin har 5.

Wadanda aka nada din sun hada da:

NIMR – Prof Babatunde Salami

NACA – Dr Sani Aliyu

NHIS – Prof Usman Yusuf

NPHCDA – Prof Echezona Ezeanolue

CDC – Dr Chikwe Andreas Ihekweazu

 

Sanarwar ta cigaba da cewa dukkan nade-naden sun fara aikin tuni.

A baya dai nade-naden da fadar shugaban kasar ke yi kan jawo kace-nace daga bangarori da dama na kasar nan inda wasu ke zargin shugaba Buharin da yin son kai wajen nade-nade wajen na mafiyancin mutane daga arewacin kasar nan.

Tuni dai fadar ta shugaban kasar ta karyata hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel