Indonesia ta zartar da hukuncin kisa kan ‘yan Nigeria

Indonesia ta zartar da hukuncin kisa kan ‘yan Nigeria

-Wasu ‘yan Najeriya su uku sun bakunci lahira a Indonisiya

-An same su da laifin fataucin miyagun kwayoyi

-Kasar ta yi biris da kiraye-kirayen kasashen duniya na a yi musu afuwa

Indonesia ta zartar da hukuncin kisa kan ‘yan Nigeria
Igwe, daya daga cikin wadanda aka zartwa da kisa a gaban kotu Indosia

Rahotanni na cewa an zartar da hukuncin kisan ne kan ‘yan Najeriyar ta hanyar harbi, bayan da wata kotun kasar ta same su da laifin shigo da miyagun kwayoyi kasar ta kuma yanke musu hukuncin.

Indonesia ta zartar da hukuncin kisa kan ‘yan Nigeria
Daya da cikin wadanda aka zaratarwa da hukuncin kisan tare da 'yan sanda

A wani rahoto na (mujallar ofishin jakadancin) Najeriya ya ce, ‘yan Najeriyan su uku, da dan Indonisiyan daya, an harbe su ne da tsakar daren Alhamis 28 ga watan Yuli, a cewar Noor Rachman, mataimakin babban mai gabatar da kara kan manyan lafuka na kasar.

Rahoton ya ce, jami’in bai ce komai ba a kan sauran mutane 10 da aka shirya kashe su tare, amma ba a yi hakan ba, cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisan, da akwai ‘yan kasar Pakistan da Zambabwe da kuma wasu ‘yan Indonisiyan.

Rahotanni sun ci gaba da cewa, an ga motocin daukar gawa na kai-komo zuwa tsibirin Nusakambangan inda gidan yarin da ake zartar da hukuncin ya ke.

Majalisar Dinkin Duniya, da kuma Kungiyar Tarayyar Turai, da kuma kungiyar Amnesty ta kasa da kasa, duk sun roki gwamnatin Indonisiyan a kan hukuncin kisan, amma ta yi biris. An rawaito shugaban kasar Joko Widodo na cewa ya yi amanna da cewa, kasar na fuskantar wani hali na bala’i saboda yawan shan miyagun kwayoyi, don haka ne ya matsa kan amfani da kisa don shawo kan lamarin.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel