Dan wasan Najeriya Emenike ya ci kwallaye biyu a Tukiyya

Dan wasan Najeriya Emenike ya ci kwallaye biyu a Tukiyya

 

– Dan wasa Emenike Emmanuel na asalin Kasar Najeriya ya zura kwallo har biyu a wasan zuwa Gasar Champions League.

– Tsohon dan wasan na West Ham dai yana ta cin kwallaye ba kakkautawa cikin kwanakin nan.

– Emenike ya jefa ma Kungiyar sa ta Fenerbache kwallayen da suka ci a wasan su da Monaco.

Dan wasan Najeriya Emenike ya ci kwallaye biyu a Tukiyya

 

 

 

 

Duk da abin da ke faruwa a Kasar Turkiyya, tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya, Emmanuel Emenike ya ci kwallaye biyu yayin da Kungiyar sa ta Fenerbache ta ba Kungiyar Monaco kashi jiya a Kasar Turkiyya. Fenerbache tayi nasara bisa AS Monaco ne da ci 2-1 a gida a wasan zuwa Gasar Champions League. Dam wasa Emenike ya zura kwallon farko ne a minti na 39, sai dai kafin a tafi hutun rabin lokaci tsohon dan wasan Man Utd da Chelsea Radamel Falcao ya ramo a minti na 42. Bayan an dawo, can da minti na 61 dan wasa Emenike ya kara jefa wani kwallon. Hakan dai yana nufin Kungiyar ta Fernabache da ke Garin Istanbul ta jefa kafa daya cikin gasar Uefa Champions League na Nahiyar Turai. Kungiyoyin za su kara fafatawa ne a mako mai zuwa, domin tantance wanda zai samu zuwa Gasar Champions league na wannan shekara.

KU KARANTA: YAN WASA BIYAR MASU TASOWA A INGILA

Tsohon dan wasan na CKSA Moscow ya dawo Kungiyar ta Fernabache ne wannan kakar, bayan ya je aro Ingila a Kungiyar West Ham. Dawowan dan wasan gaban Emenike, zuwa yanzu ya ci kwallaye har 3 a wasannin yada zangon da ake bugawa kafin a shiga Gasar wasanni. Tun bayan dai da dan wasa Emenike ya ajiye kwallo a Kasar sa ta Najeriya, ya dukufa wajen maida hankali ga bangaren Kungiyyoyin kulobs din da yake bugawa.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel