Gwamna Okowa ya kai ziyarar karshe ga Marigayi Keshi

Gwamna Okowa ya kai ziyarar karshe ga Marigayi Keshi

 

– Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta ya kai ziyarar karshe ga Marigayi Stephen Keshi

– Gwamnan na Jihar Delta ya kira iyalan Marigayin da su zama masu hakuri yayin da ake bikin birne mamacin.

– Za a birne Marigayi Keshi a Ranar Juma’a 29 ga watan Yuli a gidan sa da ke Garin Illa.

Gwamna Okowa ya kai ziyarar karshe ga Marigayi Keshi

 

 

 

 

 

 

An dai fara shirye-shiryen birne tsohon Kocin Super Eagles na Najeriya, Stephen Keshi a Jihar sa ta Delta. An fara da yi wa Marigayin addu’a ne a Cocin Katolika na St. Paul da ke Benin. Gwamnan Jihar na Delta, yayi kira ga iyalan mamacin da su zama masu hakuri kuma da godewa Ubangiji. Gwmna Okowa yana cikin wadanda suka sanya hannu bisa wani littafi na ta’aziya ga mamacin. Gwamna Okowa na Jihar yayi wannan kira ne a Ranar Laraba 27 ga Wata bayan da ya jagoranci sauran yan majalisar zartarwa na Jihar zuwa ta’aziyya ga iyalan Marigayin a gidan su da ke Garin Illa, a Karamar Hukumar Oshimili-Ta Arewa. ‘Ya ‘yan Marigayin da kuma babban kanin sa suka karbi Gwamna Okowa na Jihar da sauran tawagar sa.

KU KARANTA: AN SHIRYA JANAIZAR MARIGAYI STEPHEN KESHI

Gwamna Okowa yake cewa da dangin Marigayi Keshi; “Na zo ne tare da yan majalisar Jihar, da kuma na Tarayya da ma Majalisar zartarwa na domin ta’aziyya gare ku. Na san zafin mutuwa musamman irin wannan. Marigayi Keshi ba a kwallon kafa kadai ya bar tarihi ba, mutumin kirki ne a rayuwar sa. Ba yadda za muyi face mu rungumi kaddarar Ubangiji. Ku cigaba da addu’a ga mai duka. Mahaifin ku mutumin kirki ne, ya kuma taimaka wajen cigaban kasar sa. Marigayi Keshi namu ne duka, dan mu ne…

Gwamna Okowa na Jihar yayi alkwari ba za a taba mantawa da Marigayi Stephen Keshi ba. Ya bayyana cewa ana shirin canzawa filin wasan kwallon kafar da ke Asaba suna zuwa na Marigayin saboda gudumawar sa. Za a dai bizne Marigayi Keshi a ranar Juma’a 29 ga wannan wata.

 

Source: Legit

Online view pixel