Kwana sun kare: An kawo gawar Marigayi Stephen Keshi

Kwana sun kare: An kawo gawar Marigayi Stephen Keshi

LABARAN CIKIN GIDA

 

Kwana sun kare: An kawo gawar Marigayi Stephen Keshi

 

 

 

 

 

Daruruwan mutane na cike da hawaye yayin da aka iso da gawar Marigayi kocin Najeriya Stephen Keshi Garin Asaba na Jihar Delta domin birnewa. An dai kawo gawar Marigayi Keshi ne babban Birnin Jihar ta Delta a ranar Alhamis dinnan 28 ga wannan wata. An dai yi ‘yan wake-wake na makoki a cocin St. Paul na Katolika da ke Birnin Benin din a ranar da aka iso da gawar. An kawo gawar Marigayi Keshi ne babban dakin taro na garin Asaba, a jiya da kimanin 4:33 na yamma, Za kuma ayi addu’o’i da sauran ayyukan ibada ga mamacin a cocin St. John na Katolika da ke Garin Illah a Jihar Delta da kimanin karfe 6:00 na ranar Jumu’a. Za a wuce da gawar ne zuwa garin Illah a yau da safiya wajen karfe 7:00. Kafin nan za a tsaya da ita (gawar) a fadar Ogbelani kamar dai yadda al’adun gargajiya suka tanada da karfe 8:00 na safe. Bayan nan kuma za a garzaya gidan dangin Marigayin (Stephen Keshi) da ke Unguwar Ukpologwu a Garin Illa da karfe 8:30 na safiyar yau.

KU KARANTA: DIREBOBI SUN KASHE JAMIAN FRSC DA DAMA

Stephen Keshi ne Kocin da ya jagoranci Super Eagles ta Najeriya ta daga kofin AFCON (Watau na Zakarun Nahiyar Afrika) a shekarar 2013. Stephen Keshi ya mutu ne a Ranar 8 ga watan Yunin jiya a Garin Benin, bayan yayi fama ‘yar rashin lafiya kadan a Kafar sa. Hotuna sun nuna jama’a da dama cikin jimami da takaici na rashin wannan ta’aliki yayin da ake jiran gawar a babban dakin taro na Garin Asaba, da kuma filin wasan kwallon kafa na Garin. Mutane da dama dai sun zubar da hawaye na rashin Stephen Keshi.

 

 

Source: Legit

Online view pixel