Wata Mata Mahaukaciya Ta Samu Lafiya. 

Wata Mata Mahaukaciya Ta Samu Lafiya. 

  -Wata Mata Wacce Ta Dade A Cikin Ciwon Hauka Ta Samu Lafiya Bayan Addua'ar Da Fasto W.F Kumuyi Yayi Mata Lokacin Da Yayi Ziyarar Kwana 1 A Garin Bauchi.  

Kamar yadda Dedan Dedanson Denmark ya bayyana in da ya rubuta a shafin sa na dandalin sadarwa na facebook yace"Matar yar ya karamar hukumar Bogoro ce wadda take aiki a matsayin mai dafa abinci a makarantar Sakandare(Perfect Memorial Secondary Mauri) a kauyen Mauri ta kasance a wannan yanayin na tsawon shekara 7.

Wata Mata Mahaukaciya Ta Samu Lafiya. 

Dedan ya rubuta kamar haka"Wannan matar baza ta taba mantawa da wannan ranar ta lahadi 24/7/2016 a sauran rayuwar ta saboda a ranar ce ta warke daga cutar haukan da take ciki ta tsawon shekara 7,yayin da shahararren mutum dan yaren judea Fasto W.F Kumuyi ya mata addu'a lokacin da ya kai ziyarar kwana 1 a garin Bauci. Matar ance ita yar karamar Hukumar Bogoro ce kuma tana aiki makarantar sakandare a matsayin mai dafa abinci a kauyen Mauri, duk da yake bata san halin da take ciki ba amma yan uwanta sun bayyana mana ta shiga halin na kusan tsawon shekara 7 kuma ta zauna wurare da dama kafin daga bisani ta dawo a Rafin Zurfi a gefen hanya kusa da mahadar Benco.

KU KARANTA : A dakatar da babban taron PDP –Modu Shariff

An tattaro mana cewa wani bakanike Christopher zamani,da wata matashiya Luzar wacce ke bata abinci da wasu samari 2 da Mathew dan-dan Christopher suka saka ta a Mota suka kaita bayan filin wasan ATB Bauchi gurin da akai mata addu'a. Dan haka kada kayi shakku a kan addu'a,dan ni nagani da idona,na yarda kuma har ma nayi magana da matar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel